Lauya Abba Hikima ya bayyana cewa alakanta mutum da shan miyagun ƙwayoyi, shan giya ko kuma hauka saboda bambancin ra'ayin siyasa ba adawar siyasa ba ce, illa cin mutunci da cin zarafi.
Abba Hikima ya bayyana hakan ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, bayan ce-ce-ku-cen da suka biyo bayan sabuwar waƙar siyasa da mawaki Dauda Kahutu Rarara ya fitar, wadda wasu ke dangantawa da Farfesa Isa Ali Pantami bayan bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Jihar Gombe.
A cikin saƙon nasa, ya ce:
"Alakanta mutum da shan ƙwaya, shan giya ko hauka ba adawar siyasa ba ce. Keta mutunci ne da cin zarafi ƙarara. Idan har abin ya shafi Sheikh Pantami, ya kamata ya ɗauki matakin da ya dace. Siyasa ba hauka ba ce."
Kalaman lauyan sun jawo martani mabambanta daga masu amfani da kafafen sada zumunta.
Wasu sun goyi bayan ra'ayinsa, suna masu cewa siyasa ya kamata ta kasance kan muhawara da manufofi ba tare da cin mutuncin juna ba. Wasu kuma sun ce duk wanda ya ji an ɓata masa suna yana da damar neman hakkinsa ta hanyar doka.
Sai dai wasu masu sharhi sun yi nuni da cewa waƙar da ake magana a kanta ba ta ambaci sunan Farfesa Isa Ali Pantami kai tsaye ba, don haka suka ce ba za a iya tabbatar da cewa shi ake nufi ba.
Lamarin na ci gaba da haifar da muhawara a kafafen sada zumunta, inda ra'ayoyi suka kasu tsakanin masu ganin irin waɗannan kalamai cin mutunci ne, da kuma waɗanda ke kallonsu a matsayin wani ɓangare na zambo da habaicin siyasa.