Mawaki Soja Boy ya fitar da wani dogon bidiyo inda ya yi magana kan fitaccen jarumin Kannywood, Adam A. Zango, bayan kwanaki da ya yi alƙawarin bayyana ra'ayinsa a kansa.
A cikin bidiyon, Soja Boy ya bayyana cewa ba ya magana ne saboda ƙiyayya, sai dai saboda yana ɗaya daga cikin masoyan Adam A. Zango kuma yana ganin lokaci ya yi da zai faɗi abin da yake ɗauka a matsayin gaskiya.
Ya ce:
"Akwai dumbin masoyanka, kuma ni ma ina cikin masoyan."
Soja Boy ya bayyana Adam A. Zango a matsayin ɗaya daga cikin manyan taurarin Kannywood, yana mai cewa:
"Kai Rock Star ne, amma ba ka san kai Rock Star ba."
A cewarsa, Adam A. Zango na da dimbin masoya da damar da zai iya amfani da ita wajen bunƙasa aikinsa, amma yana ganin ba ya amfani da waɗannan damar yadda ya kamata.
Mawakin ya kuma yi iƙirarin cewa sun taɓa zama tare a baya, inda ya ba Adam wasu shawarwari kan yadda zai inganta wasu fannoni na rayuwarsa da aikinsa.
Sai dai furucin da ya fi jawo ce-ce-ku-ce a bidiyon shi ne inda ya ce:
"Adamu Zango, kai ne mutum na farko da ya fi kowa ɗaukaka amma ya fi kowa talauci a Kannywood."
Wannan furuci ya haifar da martani mabambanta a kafafen sada zumunta.
Wasu daga cikin masu sharhi sun ce Soja Boy ya bayyana abin da yake ganin gaskiya ne kuma cikin niyyar ba da shawara. Sai dai wasu sun soki kalaman nasa, suna masu cewa ba su da hujjar tabbatar da irin wannan iƙirari, tare da kare Adam A. Zango.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Adam A. Zango bai fitar da wata sanarwa ko martani a hukumance kan kalaman Soja Boy ba.