Fitacciyar jarumar Kannywood, Amal Umar, ta sanar da cewa za ta fito tare da shahararren jarumin Nollywood, Chidi Dike, a sabon fim mai suna Love and Fate.
Wannan shi ne karo na farko da jaruman biyu za su haɗu a fim guda, lamarin da ya jawo farin ciki da ɗokin gani a tsakanin masoya fina-finan Kannywood da Nollywood.
Kamfanin Amal Motion Pictures ya bayyana jerin jaruman da za su fito a fim ɗin, inda aka ga sunan Chidi Dike tare da Amal Umar, abin da ya ƙara jan hankalin masu sha'awar fina-finai.
Kasancewar Chidi Dike ba kasafai yake fitowa a fina-finan Kannywood ba, haɗin gwiwarsa da Amal Umar ya haifar da ce-ce-ku-ce da kuma hasashe cewa fim ɗin zai samu karɓuwa sosai daga masu kallo.
Masoya Amal Umar sun bayyana farin cikinsu a shafukan sada zumunta, inda da dama suka ce suna ɗokin ganin yadda haɗin gwiwar jaruman biyu zai kasance a wannan sabon shiri.
Fim ɗin Love and Fate na daga cikin sabbin ayyukan Amal Motion Pictures, bayan fina-finai irin su Safeera, Mijina da Majnoon, waɗanda suka samu karɓuwa daga masu kallo.
Yayin da ake jiran fitowar fim ɗin, ana sa ran haɗuwar Amal Umar da Chidi Dike za ta kasance ɗaya daga cikin manyan abubuwan da za su ɗauki hankalin masana'antar fina-finai ta Najeriya.