Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Alhaji Ibrahim Aliyu, ya rasu bayan fama da jinya, kamar yadda iyalansa suka tabbatar.
Marigayin, wanda ya riƙe muƙamin Mataimakin Gwamna a zamanin tsohon Gwamnan Jihar Kebbi, Sa'idu Usman Ɗakingari, tsakanin shekarun 2007 zuwa 2015, ya rasu ne a birnin Sakkwato.
Gwamnan Jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris, ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga Masarautar Yauri, Jihar Kebbi da kuma Najeriya baki ɗaya.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Gwamna Shawara na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama'a, Yahaya Sarki, ya fitar.
Gwamna Nasir Idris ya bayyana marigayin a matsayin ɗaya daga cikin fitattun shugabannin jihar, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al'umma hidima cikin gaskiya, riƙon amana da kishin ci gaban jama'a.
Ya ce marigayin ya yi fice a matsayinsa na gogaggen ma'aikacin gwamnati da Mataimakin Gwamna, inda ya samu karɓuwa da girmamawa saboda tawali'unsa da jajircewarsa wajen bunƙasa Jihar Kebbi.
Gwamnan ya ƙara da cewa Ibrahim Aliyu ya bar kyakkyawan tarihi na nagartaccen shugabanci da hidimar jama'a, wanda zai ci gaba da zama abin koyi ga al'ummomi masu zuwa.
A cewarsa:
"Gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban jiharmu da kuma jajircewarsa wajen kyautata rayuwar al'umma za su ci gaba da zaburar da al'ummomi masu zuwa."
Gwamna Nasir Idris ya yi addu'ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdausi.
Haka kuma, ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin, Masarautar Yauri da ɗaukacin al'ummar Jihar Kebbi, tare da roƙon Allah Ya ba su haƙurin jure wannan babban rashi.