Babbar Kotun Jihar Kano da ke kan titin Miller ta yanke wa wata sabuwar amarya, Saudat Idris, hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan ta same ta da laifin kashe mijinta, Salisu Idris, kwanaki tara kacal bayan ɗaurin aurensu.

Da take yanke hukuncin, Mai Shari'a Maryam Sabo ta ce kotun ta gamsu cewa masu gabatar da ƙara sun tabbatar da tuhumar da ake yi wa wadda ake zargi ba tare da wata shakka ba.

Alƙaliyar ta bayyana cewa hujjojin da lauyan gwamnatin jihar, Barista Lamido Abba Soran Ɗinki, ya gabatar, ciki har da shaidun mutane biyu da suka ba da shaida a gaban kotu, sun tabbatar da laifin kisan kai.

Bisa haka, kotun ta same ta da laifin kisan kai tare da yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya, kamar yadda doka ta tanada.

Da yake magana da manema labarai bayan yanke hukuncin, lauyan gwamnati, Barista Lamido Abba Soran Ɗinki, ya bayyana gamsuwarsa da hukuncin kotun, yana mai cewa an yi adalci bisa hujjojin da aka gabatar a lokacin shari'ar.

Sai dai lauyan da ke kare Saudat Idris ya ce ba su gamsu da hukuncin ba, kuma za su ɗaukaka ƙara zuwa kotun da ke da ikon sauraron ƙorafi domin a sake duba shari'ar.

A halin yanzu, hukuncin kotun na farko yana nan daram, sai dai shari'ar na iya ci gaba idan kotun ɗaukaka ƙara ta karɓi ƙorafin masu kare wadda aka yanke wa hukunci.