Mahaifiyar wata yarinya mai shekara takwas ta buƙaci a tabbatar da adalci bayan zargin cewa wani jami'in Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ya yi wa 'yarta fyaɗe a Jihar Bauchi.

Lauyan mai shigar da ƙara, Barista Alƙasim Mohammed, wanda ke wakiltar ƙungiyar African Child Development and Human Right Protection, ya bayyana cewa mahaifiyar yarinyar na damuwa da jinkirin gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu.

A cewar lauyan, lamarin ya faru ne lokacin da aka aika yarinyar sayo ruwan leda a gidan maƙwabcinsu, inda ake zargin wani jami'in NDLEA mai suna Muhammad Mustapha Makama ya yaudare ta sannan ya aikata laifin.

Ya ce mahaifiyar yarinyar, Salamatu Musa, ta kai rahoton lamarin ga Rundunar 'Yan Sandan Jihar Bauchi a ranar 5 ga Yulin 2026, bayan abin da ya faru.

Rahotanni sun nuna cewa bayan kama wanda ake zargin, ya shafe kusan makonni uku a tsare, amma har yanzu ba a gurfanar da shi a gaban kotu ba.

Saboda haka, ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta rubuta ƙorafi ga Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Bauchi, tana neman a gaggauta gurfanar da wanda ake zargin domin shari'a ta yi aikinta.

Barista Alƙasim Mohammed ya yaba wa jami'an 'yan sanda bisa kama wanda ake zargin, amma ya yi zargin cewa akwai wasu masu ruwa da tsaki da ke ƙoƙarin ganin an sake shi ba tare da ya fuskanci shari'a ba.

Ya kuma bayyana cewa Babban Lauyan Jihar Bauchi kuma Kwamishinan Shari'a ya riga ya bayar da shawarar shari'a, inda ya tabbatar da cewa akwai isassun hujjoji da rahoton likita da ke goyon bayan gurfanar da wanda ake zargin.

Da aka tuntubi Kakakin Rundunar 'Yan Sandan Jihar Bauchi, SP Nafiu Habib, ya tabbatar da kama wanda ake zargin, yana mai cewa za a gurfanar da shi a gaban kotu nan ba da jimawa ba.

Lura: Wanda ake zargi na ci gaba da kasancewa wanda ake zargi ne kawai, kuma doka tana ɗaukarsa a matsayin marar laifi har sai kotu ta tabbatar da akasin haka.