Ministan Kuɗin Najeriya, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa mafi yawan kuɗaɗen da gwamnati ta samu bayan cire tallafin man fetur da gyaran tsarin canjin kuɗaɗen waje suna tafiya ne wajen biyan bashin gwamnati da kuma gudanar da ayyukan gwamnati da suka ƙaru.
Ya bayyana hakan ne yayin da ake ci gaba da muhawara kan tasirin sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta fara aiwatarwa tun a shekarar 2023, waɗanda suka haifar da hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa ga al'umma.
Da yake jawabi a taron African Emerging Markets Forum da aka gudanar a Abuja, Oyedele ya ce kafin cire tallafin, tallafin man fetur da kuma abin da ya kira tallafin canjin kuɗaɗen waje suna cin kusan kashi 5 cikin 100 na kuɗaɗen shiga na gwamnati.
A cewarsa, bayan cire tallafin, wani babban ɓangare na kuɗaɗen da aka samu ya koma wajen biyan basussuka, saboda kuɗin ruwa kan lamunin gwamnati ya tashi daga kusan kashi 8 cikin 100 zuwa kashi 24 cikin 100.
Ministan ya kuma bayyana cewa gwamnatin ta ninka kuɗaɗen albashin ma'aikata bayan amincewa da sabon mafi ƙarancin albashi na naira 70,000 a wata, tare da ƙara kashe kuɗi kan shirin rancen ilimi, wanda ke biyan kuɗin makaranta da kuma tallafin rayuwa ga sama da dalibai miliyan 1.5.
Sai dai Oyedele ya yi watsi da rahoton Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) da ya nuna cewa miliyoyin 'yan Najeriya na ci gaba da rayuwa cikin talauci duk da waɗannan sauye-sauyen tattalin arziki.
A cewarsa, raguwar ƙarfin sayen kuɗin jama'a wani sakamako ne na ɗan lokaci da ba za a iya kauce masa ba bayan cire tallafin, yana mai jaddada cewa gwamnati na sa ran alfanun sauye-sauyen za su bayyana a nan gaba.