Rahotanni sun bayyana cewa wasu da ake zargin mayaƙan ƙungiyar Islamic State in the Greater Sahara (ISGS) sun yi garkuwa da wani ɗan ƙasar Jamus mai asalin Turkiyya a yankin Tahoua da ke tsakiyar Jamhuriyar Nijar.
A cewar rahotanni, mutumin ya isa birnin Niamey daga Algiers, kafin ya nufi yankin Tahoua domin gudanar da harkokin kasuwancin zinariya. Ana zargin cewa mayaƙan ISGS sun tare shi a hanya tare da yin garkuwa da shi.
Rahoton ya kuma ce masu garkuwar sun tuntubi iyalansa domin sanar da su cewa suna tsare da shi.
Lamarin ya faru ne duk da ci gaba da hare-haren soji da gwamnatin Nijar tare da ƙawayenta na Ƙawancen Ƙasashen Sahel (AES) ke kai wa ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi domin ƙwato yankunan da suke iko da su.
Sai dai matsalar tsaro na ci gaba da ƙamari a sassa daban-daban na ƙasar, musamman yankunan da ke kan iyaka, inda ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ke ci gaba da kai hare-hare da kuma gudanar da ayyukansu.
Yankin Tahoua, wanda ke da muhimmanci wajen kasuwanci da haƙar ma'adinai, na daga cikin wuraren da matsalar tsaro ta fi tsanani a Jamhuriyar Nijar.