Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ƙi amincewa da buƙatun masu garkuwa da mutanen da suka sace ɗalibai da malamai a hare-haren da aka kai makarantu uku a jihar Oyo a ranar 15 ga Mayu.
A cewarsa, maimakon yin sulhu da masu garkuwa ko biyan kuɗin fansa, gwamnati ta mayar da hankali ne kan aikin ceto ta hanyar amfani da bayanan sirri da haɗin gwiwar jami’an tsaro.
Tinubu ya bayyana hakan ne a karon farko tun bayan da aka ceto ɗalibai da malamai 39 a ranar 10 ga Yuli, yayin da yake ganawa da tawagar sarakunan gargajiya daga jihar Oyo a Abuja.
Shugaban ƙasar ya ce masu garkuwar sun buƙaci gwamnatin ta saki wasu daga cikin mambobinsu da aka kama, tare da biyan kuɗin fansa domin a sako waɗanda suke tsare da su.
“Mun ƙi tattaunawa kan biyan kuɗin fansa. Sun kuma buƙaci mu saki wasu daga cikin 'yan ƙungiyoyinsu da aka kama. Mun ce babu wata yarjejeniya. Ba za mu tattauna da masu aikata laifi ba,” in ji Tinubu.
Ya ƙara da cewa gwamnati ta himmatu wajen murƙushe masu aikata irin waɗannan laifuka tare da ɗaukar matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
Haka kuma, Tinubu ya danganta ƙaruwar sace-sacen mutane da hare-haren masu ɗauke da makamai a Najeriya da matsalolin tsaro da ke ci gaba da addabar ƙasashen yankin Sahel, yana mai cewa gwamnatin tarayya na ƙara ƙaimi wajen magance waɗannan barazanar tsaro.