Dakarun Runduna ta 4 ta Sojojin Najeriya sun yi nasarar kuɓutar da fararen hula 14 daga hannun masu garkuwa da mutane bayan wani samame da suka kai a yankunan da ke kusa da babbar hanyar Lagos–Benin a jihar Edo.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Kyaftin Kennedy Anyanwu, ya fitar, ya ce dakarun sun gudanar da aikin ne ƙarƙashin samamen Operation WABAIZIGAN, kwana guda bayan harin da masu garkuwa suka kai kan matafiya a babbar hanyar.

Sanarwar ta ce sojojin sun kai samamen ne a hanyoyi da dazukan ƙaramar hukumar Ovia North East da ke jihar Edo, bayan samun sahihan bayanan sirri da misalin ƙarfe 9:30 na dare, wanda ya ba su damar gano hanyar da masu garkuwar ke bi.

A cewar rundunar, matsin lambar da dakarun suka yi ya tilasta wa masu garkuwar barin mutum 11 daga cikin waɗanda suka sace tare da tserewa cikin daji.

Sai dai sojojin ba su dakatar da aikin ba, inda suka ci gaba da wani samame da safiyar ranar Juma'a, wanda ya kai ga kuɓutar da sauran mutum uku, lamarin da ya sa adadin waɗanda aka ceto ya kai 14.

Rundunar ta ce a halin yanzu dakarunta na ci gaba da gudanar da wani samame na musamman domin gano tare da cafke masu garkuwar da suka tsere.