Tsagin jam'iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Kabiru Turaki ya sanar da cewa ya miƙa sunan tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a matsayin ɗan takararsa na shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027.

Kakakin kwamitin riƙon ƙwaryar tsagin, Ini Ememobong, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja.

A cewarsa, rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam'iyyar PDP bayan hukuncin Kotun Ƙoli ne ya sa aka kafa kwamitin riƙon ƙwarya domin tafiyar da harkokin jam'iyyar da kuma gudanar da muhimman ayyukanta.

Tsagin ya jaddada cewa shi ne halastaccen shugabancin PDP, kuma shi ne ya amince da tsayar da Goodluck Jonathan a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, tare da zaɓen 'yan takarar gwamnoni da na majalisun dokoki na tarayya da jihohi.

Haka kuma, ya bayyana cewa ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke kwanan nan dangane da rikicin shugabancin jam'iyyar.

Sai dai, har yanzu ba a samu wata sanarwa daga INEC da ke tabbatar da karɓar wannan takara ba, kuma rikicin shugabanci a cikin jam'iyyar PDP na ci gaba da kasancewa a gaban kotuna.