Matar Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga Masarautar Saudiyya da ta tallafa wa Najeriya wajen faɗaɗa damar samun ilimin zamani ga almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta, tana mai cewa hakan zai taimaka wajen rage matsalolin rashin tsaro da inganta makomar ƙasar.
Oluremi Tinubu ta bayyana hakan ne yayin da ta karɓi baƙuncin Jakadan Saudiyya a Najeriya, Yousef Mohammed Al-Balawi, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Ta ce akwai buƙatar ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Saudiyya domin inganta tsarin ilimin almajirai ta hanyar haɗa karatun addinin Musulunci da ilimin zamani, domin bai wa yara marasa galihu damar samun ingantaccen ilimi.
A cewarta, wannan tsari zai samar wa yara, musamman na yankin Arewacin Najeriya, damar samun ilimi mai inganci tare da ci gaba da koyon addininsu.
"Ina aiki da mata da yara marasa galihu, amma ina matuƙar tausayawa yara almajirai a Arewacin Najeriya. Sun cancanci samun kulawa mafi kyau," in ji Oluremi Tinubu.
Ta kuma yi gargaɗin cewa idan ba a magance matsalar almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta ba, hakan na iya ƙara ta'azzara matsalolin tsaro a ƙasar.
A cewarta, samar da ilimin zamani tare da na addini ga waɗannan yara zai taimaka wajen gina makoma mai cike da zaman lafiya da ci gaba ga Najeriya.