Gwamnatin Jihar Kano ta miƙa takardun mallakar filaye (Certificate of Occupancy – C of O) ga masu bai wa gwamna shawara da kuma masu ɗauko rahoto daga ma'aikatu, a wani biki da aka gudanar a Coronation Hall da ke Gidan Gwamnatin Kano.

Bikin ya samu halartar manyan jami'an gwamnati da kuma waɗanda suka amfana da shirin.

Da yake jawabi a wajen taron, Kwamishinan Ƙasa da Tsare-tsare na Jihar Kano, Abduljabbar Muhammad Umar, ya ce gwamnatin jihar ta aiwatar da shirin ne domin cika alƙawarin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauka ga mukarraban gwamnatinsa.

Ya bayyana cewa an gudanar da aikin tantance masu cin gajiyar shirin tare da fitar da takardun mallakar filayen ne bisa ƙa'idoji da tsarin doka, domin tabbatar da gaskiya da adalci wajen rabon filayen.

Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da aiwatar da manufofin da ke inganta walwalar ma'aikata da masu ba ta gudunmawar gudanar da ayyukan gwamnati.