Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ba ta da wani shiri na ƙara kuɗin wutar lantarki a halin yanzu, tana mai jaddada cewa abin da ta fi bai wa muhimmanci shi ne inganta samar da wutar lantarki da kuma bunƙasa ayyukan ɓangaren.
A cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, ya ambato Ministan Lantarki, Joseph Tegbe, yana cewa gwamnatin na mayar da hankali ne kan ƙara yawan wutar lantarki, samar da mitoci ga masu amfani da wuta, da kuma tabbatar da cewa ana biyan kuɗin wutar da aka yi amfani da ita.
Kalaman ministan sun zo ne bayan damuwar da jama'a ke ci gaba da nunawa kan tsadar kuɗin lantarki, musamman bayan sauye-sauyen farashin da aka yi a baya ga masu amfani da wutar Band A.
Ministan ya ce:
"Ba mu da wata manufa ta ƙara kuɗin lantarki fiye da yadda yake a yanzu. Burinmu shi ne inganta samar da wutar lantarki, tabbatar da kowa ya samu mita, sannan 'yan Najeriya su riƙa biyan kuɗin wutar da suka yi amfani da ita."
Ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da nazarin hanyoyin da za su kare muradun masu amfani da lantarki, musamman a yankunan da har yanzu ba sa samun isasshiyar wuta, tare da ɗaukar wasu matakan da za su inganta ayyukan fannin lantarki a faɗin ƙasar.