Rundunar Sojojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation Hadin Kai sun kama mutum shida da ake zargi da taimaka wa mayaƙan ƙungiyar ISWAP wajen gudanar da ayyukansu a Damasak, Jihar Borno.

A cikin wata sanarwa, rundunar ta ce an kama waɗanda ake zargin ne a ranar 27 ga Yulin 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri da suka nuna cewa suna taimaka wa ƙungiyar ta hanyar samar mata da kuɗaɗe ta hanyar saye da sayar da shanu a kasuwannin Gubio, Damasak da Ajuwango.

Rundunar ta bayyana cewa yayin samamen, dakarun sun ƙwace makamai, mota, da kuma kuɗi har Naira 317,950 daga hannun waɗanda ake zargin.

Sojojin sun ce mutanen da aka kama na ci gaba da fuskantar bincike, tare da jaddada cewa za su ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin lalata hanyoyin samar da kuɗi da kayan aiki ga ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.