Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa matar wani babban jami'in kula da harkokin kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP, tare da ɗanta mai shekara 11, sun miƙa wuya ga dakarun Operation Hadin Kai a ƙauyen Kusuma da ke Jihar Borno.
A cikin wata sanarwa, rundunar ta ce binciken farko ya nuna cewa mijin matar, wanda ake bayyana a matsayin babban kwamandan ISWAP, ya miƙa wuya ga sojoji a ranar 25 ga Yuli, kuma shi ne ya umarce ta da ta fito daga maɓoyarsu tare da ɗansu domin su miƙa wuya.
Haka kuma, rundunar ta ce dakarunta sun kai wani samame na daban a yankin Turoh bayan samun sahihan bayanan sirri kan motsin mayaƙan ƙungiyar.
A cewar sanarwar, mayaƙan sun tsere kafin isowar sojojin, inda suka bar wasu kayayyaki a wurin.
Bayan binciken yankin, dakarun sun ƙwato babura biyu da kuma tarin miyagun ƙwayoyi, waɗanda ake zargin mayaƙan sun bari yayin da suke tserewa.
Rundunar ta jaddada cewa za ta ci gaba da gudanar da hare-hare da suka dogara da sahihan bayanan sirri domin daƙile ayyukan ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.