Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fara nuna wa jama'a takardun shaidar karatu da bayanan sirri na 'yan takarar shugaban ƙasa da mataimakansu domin babban zaɓen shekarar 2027.
Takardun da aka wallafa sun haɗa da na Shugaba Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, waɗanda jam'iyyar APC ta tsayar takara.
Bisa bayanan da INEC ta wallafa, Shugaba Tinubu ya kammala digirin farko (B.Sc.) a fannin Gudanar da Kasuwanci (Business Administration) daga Jami'ar Chicago da ke Amurka a shekarar 1979.
Takardun sun kuma nuna cewa ya yi hidimar bautar ƙasa (NYSC) a Jihar Oyo tsakanin 1982 zuwa 1983, sannan ya yi aiki a Mobil Nigeria, gwamnatin Jihar Legas da kuma gwamnatin tarayya.
A ɓangaren mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, bayanan sun nuna cewa ya yi karatun firamare a Lamisula, sakandare a Government Secondary School, Potiskum, sannan ya sami digirin farko a fannin Noma daga Jami'ar Maiduguri a shekarar 1989.
Haka kuma, ya kammala digirin digirgir (M.Sc.) a fannin Tattalin Arzikin Noma daga Jami'ar Ibadan, tare da yin bautar ƙasa tsakanin 1989 zuwa 1990.
INEC ta bayyana cewa wallafa takardun ya kasance ne bisa tanadin Sashe na 29(3) na Dokar Zaɓe ta 2026, wanda ya wajabta a bai wa jama'a damar duba bayanan 'yan takara.
A cewar hukumar, duk wani da ke da hujjar cewa ɗan takara ya bayar da bayanan ƙarya ko takardun bogi na iya ɗaukar matakin shari'a kamar yadda doka ta tanada.
Hukumar ta kuma sanar da cewa yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisun dokoki na tarayya zai fara ne a ranar 19 ga Agustan 2026.