Rundunar Sojin Najeriya ta ce wasu mayaƙa a yankin Kudu maso Gabas sun fara ajiye makamansu da kansu sakamakon matsin lambar da dakarun soji ke ci gaba da yi musu.
Rundunar ta bayyana cewa hakan ya biyo bayan jerin samame da hare-haren da aka kai maboyar mayaƙan, musamman bayan kama wasu da ake zargi da hannu a kisan wani jami’in soja.
A cewar sojojin, ɗaya daga cikin waɗanda aka kama ya jagoranci jami’an tsaro zuwa wani wurin da aka ɓoye makaman ƙungiyar a yankin Egbema da kewaye, inda aka gano tare da ƙwato bindigogi, harsasai da sauran kayan yaƙi.
Rundunar ta ce wannan ci gaban na nuna cewa hare-haren da take kai wa masu tayar da zaune tsaye na ci gaba da raunana ƙarfinsu, tare da tilasta wa wasu daga cikinsu yin watsi da ayyukan ta'addanci da kuma miƙa makamansu.