Rundunar Sojin Ruwan Najeriya ta ce ta gano wata matatar man fetur ta bogi tare da ƙwace kimanin lita 87,000 na dizel da ake zargin an tace ba bisa ƙa'ida ba a Jihar Rivers.
A cewar rundunar, an gudanar da wannan samame ne a wani ɓangare na yaƙin da gwamnati ke ci gaba da yi da satar ɗanyen mai da kuma tace shi ba bisa doka ba a yankin Neja Delta.
Kakakin rundunar, Kyaftin Abiodun Folorunso, ya bayyana cewa an gano wurin na ɗauke da dizel da ake zargin an tace ba bisa ƙa'ida ba, tare da tankunan ajiya da sauran kayan aikin da ake amfani da su wajen sarrafa kayayyakin man fetur ba bisa doka ba.
Ya ce aikin ya kai ga ƙwato kimanin lita 87,000 na dizel, inda aka kuma ɗauki duk matakan da suka dace wajen adana man da aka ƙwato da sauran kayayyakin da aka samu, bisa ƙa'idojin rundunar.
Rundunar Sojin Ruwan Najeriya ta jaddada cewa za ta ci gaba da ƙarfafa yaƙi da satar mai da kuma kare muhimman kadarorin tattalin arzikin ƙasa.