Aƙalla mutum biyar ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 41 suka ɓace bayan wani jirgin ruwa ɗauke da sama da fasinjoji 250 ya kama da wuta a tekun Indonesia.
Hukumar Ceto ta Ƙasa ta Indonesia ta bayyana cewa jirgin, mai suna KMP Mutiara Sentosa 2, ya kama da wuta ne yayin da yake tafiya daga birnin Surabaya na lardin Gabashin Java zuwa Makassar a lardin Sulawesi ta Kudu.
Rahotanni sun nuna cewa fasinjoji da dama sun sanya rigunan ceton rai, yayin da wasu suka yi tsalle cikin teku domin gujewa gobarar da ta bazu a mafi yawan sassan jirgin.
Jami'an ceto na ci gaba da aikin neman waɗanda suka ɓace tare da ceto sauran fasinjojin da abin ya shafa.
Har yanzu dai ba a bayyana musabbabin tashin gobarar da ta rutsa da jirgin ba, yayin da bincike ke ci gaba.