Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation UDOKA sun kama wasu manyan mambobin wata ƙungiyar masu aikata laifuka da ake zargi da kai wa sojoji kwanton ɓauna a ranar 4 ga Mayun 2026 a Jihar Delta.

Rundunar ta ce harin ya yi sanadin mutuwar soja guda ɗaya tare da jikkata wani.

A cikin wata sanarwa, sojojin sun bayyana cewa bayan harin ne suka ƙaddamar da jerin samame bisa bayanan sirri domin kamo waɗanda ake zargi da kuma ƙwato makaman da aka sace.

Samamen ya kai ga cafke mutane uku da aka fi sani da laƙabban Chiboy, Marathon da Onowu, bayan sun tsere zuwa garin Oleh da ke Jihar Delta.

Sojojin sun ƙara da cewa waɗanda aka kama sun jagoranci jami'an tsaro zuwa maɓoyarsu da ke Aggah Plantation a Jihar Rivers da kuma Umudike Plantation, inda aka gano tare da ƙwato makaman da aka sace da sauran kayan aikin da ake zargin ana amfani da su wajen aikata laifuka.

An ce a yayin samamen an ƙwato bindigogi, alburusai da sauran kayan yaƙi.

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ana ci gaba da bincike kan waɗanda ake zargin kafin gurfanar da su a gaban kotu, tare da jaddada ƙudurinta na ci gaba da yaƙi da masu aikata laifuka domin tabbatar da zaman lafiya a yankin.