Masu harkar hawa tsaunuka a sassa daban-daban na duniya na alhini bayan rasuwar fitaccen mai hawan tsaunuka, Nirmal Purja, tare da wasu mutum tara sakamakon zaftarewar ƙanƙara a Dutsen Broad Peak da ke Pakistan.
Purja, ɗan asalin Nepal mai ɗan ƙasar Birtaniya, kuma tsohon jami'in rundunar musamman ta sojin Birtaniya, ya rasu yana da shekara 43.
Ministan Tsaron Birtaniya, Wes Streeting, ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai jajircewa da ƙarfafa gwiwa, wanda ya sadaukar da shekaru da dama yana yi wa ƙasar hidima.
Shi ma Firaministan Nepal, Balendra Shah, ya ce rasuwar Purja da sauran waɗanda abin ya shafa babban bala'i ne da ya girgiza al'ummar ƙasar.
Jami'ai sun ce ya zuwa yanzu an gano gawarwaki uku ne kawai daga cikin mutum goma da hadarin ya rutsa da su.
Sun kuma bayyana cewa gawar Nirmal Purja da ta sauran masu hawan tsaunukan na wani wuri ne mai matuƙar wahalar isa, kuma har yanzu ba a kai ga kwaso su ba.