Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab'i ta Jihar Kano ta rufe shagon wani mashahurin mai sayar da magungunan gargajiya, Kausar Unique Empire Ltd, wanda aka fi sani da Kausar Mai Back to Back, bisa zargin amfani da kalamai da hotunan batsa wajen tallata hajojinsa a kafafen sada zumunta.

A cikin wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar a madadin shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, an ce matakin ya biyo bayan bayanan sirri da kuma korafe-korafen da jama'a suka kai wa hukumar.

Sanarwar ta ce sashen sa ido kan masu sayar da magungunan gargajiya ne ya gano laifukan, inda ya ɗauki matakin rufe shagon cikin gaggawa bayan tabbatar da zargin.

Hukumar ta bayyana cewa irin waɗannan tallace-tallace sun saɓa wa dokokin da ke tsara tallata magungunan gargajiya, tare da yin karo da al'adu da ɗabi'un al'ummar Jihar Kano.

Haka kuma, ta yi gargaɗi ga sauran masu sana'ar sayar da magungunan gargajiya da su tabbatar da cewa hanyoyin tallata hajojinsu sun dace da ƙa'idojin doka da kuma kyawawan ɗabi'un al'umma.