Aƙalla mutum takwas ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren sama da Isra'ila ta kai cikin dare a sassa daban-daban na Zirin Gaza, kamar yadda jami'an Falasɗinawa suka bayyana.

Hukumar Kare Fararen Hula ta Gaza ta ce hare-haren sun afku ne a Gaza City, Khan Younis da Deir el-Balah, inda aka kai hare-hare kan wasu gine-ginen zama.

A nata ɓangaren, Sojojin Isra'ila (IDF) sun ce sun kai hare-haren ne kan mayaƙan Hamas, tare da iƙirarin kashe kwamandoji biyu na ƙungiyar, ciki har da ɗaya daga rundunar Nukbha da kuma wani daga Bataliyar Maghazi.

Rahotanni sun nuna cewa daga cikin waɗanda suka mutu akwai wani yaro, da kuma wasu 'yan uwa uku da suka rasa rayukansu bayan wani hari da aka kai kan gidansu a Khan Younis.

Sabbin hare-haren na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Hamas ta bayyana amincewarta da wani shirin kwance ɗamara, yayin da Isra'ila ke cewa har yanzu ba a cimma wata yarjejeniya ta tsagaita wuta a Zirin Gaza ba.