Aƙalla mutum 18, ciki har da sojoji huɗu, sun rasa rayukansu bayan wasu 'yan bindiga sun kai hare-hare a wasu al'ummomi da ke jihohin Zamfara da Sakkwato, a Arewa maso Yammacin Najeriya.
A Jihar Zamfara, mazauna ƙauyen Kasuwar Daji sun ce maharan sun kai hari wani sansanin sojoji kafin daga bisani su kutsa cikin ƙauyen, inda suka yi garkuwa da fiye da mutum 100.
Rahotanni sun ce daga baya maharan sun saki matan da suka kama, sai dai har yanzu ana ci gaba da tsare kusan maza 52.
A Jihar Sakkwato kuwa, an ce 'yan bindigar sun shafe sa'o'i suna kai hare-hare gida-gida a ƙauyen Lajinge da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni.
Maharan sun kashe fararen hula, sun sace dabbobi tare da ƙona wasu gidaje.
Daga cikin waɗanda suka mutu akwai wani magidanci da 'ya'yansa maza biyu, waɗanda rahotanni suka ce sun ƙone da ransu yayin da suke ɓoye a cikin gidansu.
Shaidu sun kuma bayyana cewa an yi garkuwa da wasu mata biyu, yayin da hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan hare-haren ba.