Rundunar Operation FANSAN YAMMA ta ce wani jami'in soja da ɗan sanda sun rasa rayukansu yayin da suke daƙile wani hari da 'yan bindiga suka kai sansanin sojoji da ke Kasuwan Daji, a Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda ta Jihar Zamfara.
A cewar rundunar, maharan sun yi ƙoƙarin kutsawa cikin sansanin da misalin ƙarfe 1:40 na safiyar ranar 2 ga Agusta, amma dakarun da ke wurin sun gano yunƙurin tun da wuri tare da mayar da martani, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa.
Bayan artabun, ƙarin dakaru sun bi sahun maharan, inda suka samu nasarar kuɓutar da mutum tara daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su a lokacin harin.
Rundunar ta kuma bayyana cewa sojoji biyu sun jikkata sakamakon harbin bindiga, kuma an garzaya da su asibiti domin samun kulawar likitoci.
Haka kuma, ta ƙaryata rahotannin da ke cewa jami'an tsaro shida ne suka mutu, tana mai jaddada cewa jami'in soja guda ɗaya da ɗan sanda guda ɗaya ne kaɗai suka rasa rayukansu a harin.