Hukumar shari'ar Iran ta sanar da aiwatar da hukuncin kisa kan Omid Behzad da Pouria Safvat a safiyar Litinin, bayan kotu ta same su da laifin yi wa Isra'ila leƙen asiri.
A cewar kamfanin yaɗa labarai na ma'aikatar shari'ar Iran, Mizan, mutanen biyu sun kasance suna tattarawa tare da aika wa hukumar leƙen asirin Isra'ila, Mossad, bayanai, hotuna da kuma bayanan wuraren da cibiyoyin soji da na tsaron Iran suke.
Mahukuntan Iran sun ce bayanan da aka tattara sun taimaka wajen gudanar da ayyukan leƙen asiri da suka shafi tsaron ƙasar.
Sai dai ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama da wasu lauyoyi sun dade suna nuna damuwa kan yadda ake gudanar da irin waɗannan shari'o'i a Iran, suna zargin cewa ana aiwatar da hukuncin kisa cikin gaggawa ba tare da tabbatar da cikakken tsarin shari'a mai adalci ba.
Sun kuma bayyana cewa rashin bai wa waɗanda ake tuhuma damar samun cikakkiyar kariyar doka da kuma lauya yadda ya kamata na daga cikin abubuwan da ke haifar da tambayoyi kan adalcin irin waɗannan hukunci.