Taron ya gudana ne a ƙarƙashin jagorancin shirin Drug Abuse Awareness Campus Tour (DAACT), wanda ke yaƙi da wayar da kai kan illar shaye-shaye a jami'o'in ƙasar nan. An gudanar da shi a ɗakin taro na Hafizu Abubakar da ke jami'ar North West University, Kano.
Da yake jawabi, shugaban SEYDI na shiyyar Arewa, Dr. Aliyu Bello Jikantoro, ya bayyana cewa an zaɓi jami'ar North West University ne saboda rahotanni da ke nuna cewa Jihar Kano na daga cikin jihohin da ke da yawan matasan da ke ta'ammali da miyagun ƙwayoyi a Najeriya.
Masu ruwa da tsaki da dama kan yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi sun halarci taron, ciki har da hukumar NDLEA reshen Jihar Kano. Kwamandan hukumar, Dahiru Lawal Yahaya, ya bayyana cewa yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi aiki ne na hukumar, don haka a shirye suke su ba SEYDI cikakken haɗin kai wajen gudanar da wannan aiki a jami'o'in Jihar Kano da kewaye.
Ya kuma yi kira ga ɗaliban jami'ar da su guji shaye-shaye da ta'ammali da miyagun ƙwayoyi, tare da kauce wa abokan banza domin inganta rayuwarsu.
Shugabar jami'ar North West University, Hajiya Amina Salihi Bayero, ta yabawa SEYDI bisa wannan kyakkyawan tunani na shirya gangamin wayar da kan ɗalibai. Ta ce shaye-shayen miyagun ƙwayoyi na lalata rayuwar matasa da makomarsu, kuma wannan gangami babban mataki ne na kawo ƙarshen wannan mummunar ɗabi'a. Ta ce shirin zai wayar da kan ɗalibai tare da koya musu hanyoyin kauce wa shaye-shaye, tare da ƙarfafa su su zama jakadun yaƙi da miyagun ƙwayoyi (Anti-Drug Abuse Ambassadors).
A ƙarshe, ta gode wa SEYDI da sauran masu ruwa da tsaki da abokan hulɗa bisa wannan ƙoƙari na yaƙi da shaye-shaye da ta'ammali da miyagun ƙwayoyi tsakanin matasan jami'ar.
A nasa jawabin, Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Makoda, wanda Comrade Sagir Danbare Umar ya wakilta, ya ce gwamnatin jihar ta yi matuƙar farin ciki da shirya wannan gangami, tare da yin alƙawarin ba da cikakken goyon baya domin rage yawan masu ta'ammali da miyagun ƙwayoyi a jami'o'in jihar.
Ya kuma yabawa SEYDI bisa haɗa manyan masana daga hukumomi irin su NDLEA da NAFDAC, yana mai cewa irin wannan gangami zai taimaka matuƙa wajen rage shaye-shaye tsakanin matasa.
Ɗalibai da dama sun bayyana farin cikinsu da samun damar halartar taron. Firdausi Usman Datti, ɗaliba a Jami'ar Bayero Kano, ta ce shirin zai taimaka wajen rage shaye-shaye tsakanin ɗalibai, musamman ganin cewa za a koya musu dabarun dogaro da kai da kuma yadda za su kare kansu daga gurɓatattun abokai.
Haka kuma, Ali Abdurra'uf Abubakar, ɗalibi a North West University kuma jakadan SEYDI (Campus Ambassador), ya bayyana jin daɗinsa da zuwan ƙungiyar makarantar, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen yaƙi da shaye-shaye domin ɗalibai su samu sakamako mai kyau a karatunsu.
Dr. Aliyu Bello Jikantoro ya gode wa shugabannin al'umma da hukumomi da suka amsa gayyatar taron, yana mai cewa halartar manyan baƙi ta ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da wayar da kan ɗalibai a jami'o'in Najeriya.