Gwamnatin Jihar Kano ta nemi ƴan kasuwa da masu zuba jari su saka hannun jari a fannin tsaftar muhalli domin inganta lafiyar al'umma, samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arzikin jihar.
Wannan na cikin sanarwar da Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi naJihar, Dr. Dahiru Muhammad Hashim, ya fitar.
Sanarwar ta ce Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da wani shirin haɗin gwiwa kan tsaftar muhalli da aka gudanar a otal din Porto Golf da ke Kano.
Ya ce gwamnatin jihar na kallon tsaftar muhalli a matsayin wata dama ta bunƙasa tattalin arziki, inda ya bayyana cewa akwai damar zuba jari a gine-ginen bandakunan jama'a da sarrafa najasa da cibiyoyin tace shara da kuma amfani da shara wajen samar da wasu kayayyaki masu amfani.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin jihar ta kuma ƙaddamar da shirin Smart Kano Waste and Sanitation Initiative, tare da yin kira ga masu zuba jari da cibiyoyi da su tallafa wa ayyukan tsaftar muhalli domin samar da mafita mai ɗorewa ga al'umma.