Rundunar 'Yan Sandan Jihar Borno ta kama mutane biyar kan zargin yanka matattun shanu da sayar da namansu ga ɗaiɗaikun mutane da mahauta masu tsire a birnin Maiduguri.

Wannan na cikin sanarwar da Jami'in Hulɗa da Jama'a na Rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya fitar jiya litinin.

Sanarwar ta bayyana cewa an kama waɗanda ake zargin ne a tsohuwar kasuwar shanu ta Maiduguri, bayan samun sahihan bayanan sirri, inda ake zarginsu da yanka shanun da suka mutu tare da sayar da namansu ga jama'a.

Sanarwar ta ƙara da cewa a lokacin kama su, an same su da gawar matacciyar saniya da ake zargin suna shirin kai wa yankin Morumti domin sarrafawa da rarrabawa.

Haka kuma rundunar ta bayyana cewa ana ci gaba da bincike domin gano sauran waɗanda ake zargi da hannu a lamarin, kafin a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu.