Ƙungiyar kare haƙƙin bil-adama ta ƙasa da ƙasa, ta koka kan karancin malaman da ke koyarwa a sashin larabci da nazarin addinin muslunci muslunci na jami'ar Jos.
Hukumar ta ce abin takaici ne yadda ake fuskantar koma baya a wannan bangaren, duk da hakkin da dokokin kare haƙƙin bil-adama suka yi tanadi a wannan bangare.
Daraktan ƙungiyar kare haƙƙin bil-adama ta ƙasa da ƙasa Ambasada Abdullahi Bakoji Adamu, shine ya bayyana haka a wani sakon murya da aike mana.
Ƙungiyar ta bukaci gwamanatin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki da suyi duk mai yiwuwa wajen samar da mafita kan wannan kalubale.