Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da wani ƙudiri da zai hana makarantu masu zaman kansu ƙara kuɗin makaranta ba tare da samun izini da sahalewar hukuma ba, domin kare iyaye da masu kula da yara daga ƙarin kuɗaɗe ba tare da ƙa'ida ba.

Ƙudirin gyaran Dokar Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu da na Sa-kai ta shekarar 2026 ya tanadi cewa duk wata makaranta da ke son ƙara kuɗin makaranta dole ne ta fara neman amincewar hukumar da abin ya shafa kafin aiwatar da hakan.

Rahotanni sun nuna cewa duk wani ƙarin kuɗin makaranta da ya wuce kashi 10 cikin 100 zai buƙaci ƙarin nazari da sahalewa daga hukumar.

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Ismail Falgore, ya bayyana cewa sabuwar dokar za ta taimaka wajen inganta tsarin gudanar da makarantu masu zaman kansu tare da tabbatar da kare muradun iyaye da ɗalibai.

Har ila yau, dokar ta tanadi ƙirƙirar muƙamin Sakataren Zartarwa domin ƙara inganta gudanar da ayyukan Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu da na Sa-kai.

Majalisar ta amince da ƙudirin ne bayan gudanar da zaman sauraron ra'ayoyin jama'a da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, wanda Kwamitin Ilimi na Majalisar ya jagoranta kafin gabatar da rahotonsa.