Rundunar Sojin Najeriya ta tura jami'ai 86 zuwa ƙasar Guinea-Bissau domin shiga aikin wanzar da zaman lafiya na Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS).
A cewar rundunar, matakin na nuna ci gaba da jajircewar Najeriya wajen tallafa wa zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a yankin Afirka ta Yamma.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafukanta na sada zumunta, ta bayyana cewa jami'an sun tashi daga Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, kuma sun isa Guinea-Bissau lafiya domin fara aikinsu ƙarƙashin umarnin ECOWAS.
Rundunar ta kuma jaddada cewa Najeriya na ci gaba da kasancewa cikin ƙasashen Afirka da suka fi bayar da gudunmawa wajen ayyukan wanzar da zaman lafiya na ECOWAS, Tarayyar Afirka (AU) da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya (UN).
Ta ce sabon aikin ya sake nuna muhimmiyar rawar da Najeriya ke takawa wajen hana rikice-rikice, gina zaman lafiya da dawo da kwanciyar hankali a ƙasashen Afirka.
An kafa rundunar ta ECOWAS a Guinea-Bissau ne domin tallafa wa ɓangaren tsaro da kuma inganta tsarin siyasa a ƙasar, bayan shekaru ana fama da rikice-rikicen siyasa da juyin mulkin soja.
Najeriya ta daɗe tana daga cikin ƙasashen da suka fi tura dakaru zuwa ayyukan ECOWAS, inda ta ba da gudunmawar sojoji, kayan aiki da jagoranci a ƙasashe irin su Liberiya, Saliyo, Gambiya da Guinea-Bissau.
Sai dai wannan mataki na zuwa ne a lokacin da Najeriya ke ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsaro a sassa daban-daban na ƙasar, ciki har da hare-haren 'yan bindiga, satar mutane domin neman kuɗin fansa da sauran matsalolin tsaro.