Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ingila (FA) na shirin rubuta wa shugaban FIFA, Gianni Infantino, takardar sanar da janye goyon bayan da take ba shi, yayin da yake fuskantar ƙarin matsin lamba kan shirinsa na sayar da hannun jari a gasannin FIFA ga masu zuba jari masu zaman kansu.
Matakin ya zo ne a daidai lokacin da UEFA ke barazanar ɗaukar matakin shari'a kan shirin, yayin da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Wales ita ma ta bayyana janye goyon bayanta ga yunƙurin Infantino na ci gaba da shugabancin FIFA.
Ana sa ran a watan Maris mai zuwa Infantino zai tsaya takara a karo na huɗu kuma na ƙarshe domin ci gaba da zama shugaban FIFA. Domin samun nasara, zai buƙaci kuri'u aƙalla 106 daga cikin mambobin FIFA 211.
Majiyoyi sun shaida wa BBC cewa Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Scotland (Scottish FA) na ci gaba da mara wa matsayar UEFA baya, inda take nuna rashin gamsuwa da shugabancin Infantino.
Haka kuma, hukumomin ƙwallon ƙafa na Turai da na yankin Arewacin Amurka, Tsakiyar Amurka da Caribbean (Concacaf) sun bayyana damuwarsu a fili, inda UEFA da Concacaf suka fitar da kalamai masu sukar wasu daga cikin tsare-tsaren da shugaban FIFA ke ƙoƙarin aiwatarwa.