Ƙaramin Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Sola Enikanolaiye, ya yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su ƙara wayar da kan al'umma kan ayyukan Ma’aikatar Harkokin Waje da Hukumar Nigeria Technical Aid Corps (NTAC).
Ministan ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da Darakta Janar na NTAC, Yusuf Buba Yakub, ya kai masa bayanin ayyukan hukumar a wani ɓangare na sabon shirin sake fasalin manufofin harkokin wajen Najeriya bisa tsarin 4-Ds.
A cikin wata sanarwa, Ministan ya ce a halin yanzu bayyana ayyukan gwamnati ga jama'a yana da muhimmanci kamar aiwatar da su, yana mai jaddada buƙatar samar da ingantaccen shirin sadarwa da isasshen kuɗin gudanarwa.
Ya bayyana cewa ayyukan NTAC sun ta'allaka ne kan manufar harkokin wajen Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta 4-Ds, wato Demography (Yawan Jama'a), Democracy (Dimokuraɗiyya), Development (Ci Gaba), da Diaspora ('Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje).
Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa tun bayan kafuwar NTAC a shekarar 1987, hukumar ta tura ƙwararru sama da 10,000 zuwa ƙasashe fiye da 40 domin bayar da gudunmawar fasaha da ƙwarewa.
A halin yanzu, akwai masu aikin sa-kai 274 da ke aiki a ƙasashe 13 na ƙungiyar ACP, inda suke ba da gudunmawa a fannonin lafiya, ilimi, injiniya da fasahar sadarwa (ICT).
Haka kuma, Ma’aikatar Harkokin Waje ta bayyana cewa ana ci gaba da aiwatar da sauye-sauye domin inganta ayyukanta da tabbatar da cewa suna tafiya daidai da muradun ƙasa.