Ana sa ran Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai aza harsashin fara aikin gina titin Kaduna zuwa Birnin Gwari mai tsawon kilomita 122, wani aiki da ake kallon zai zama muhimmin ci gaba ga bunƙasa ababen more rayuwa da tattalin arzikin Jihar Kaduna.

A baya, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya sanar da cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da ware Naira biliyan 178.12 domin gina hanyar. Haka kuma, an ware Naira biliyan 100 domin fara aikin ba tare da ɓata lokaci ba.

Sabuwar hanyar za ta tashi ne daga Mando da ke birnin Kaduna zuwa garin Birnin Gwari, yankin da ya daɗe yana fuskantar matsalolin lalacewar hanya da kuma ƙalubalen tsaro.

Rahotanni sun nuna cewa za a yi aikin ne da fasahar Continuously Reinforced Concrete Pavement (CRCP), wacce ke amfani da kankaren siminti mai ƙarfi da ƙarafa. Masana sun bayyana cewa irin wannan hanya na iya ɗaukar shekaru masu yawa ba tare da buƙatar manyan gyare-gyare ba.

An bayyana cewa aiwatar da wannan aikin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun ingantuwar tsaro a yankin Birnin Gwari, inda kasuwanni da dama da aka rufe a baya suka koma aiki, gonaki kuma suka fara komawa ana noma su.

Hakazalika, gwamnatin jihar na ci gaba da aikin gina hanyar Bagoma zuwa Gagumi mai tsawon kilomita 36 domin ƙara sauƙaƙa zirga-zirga da bunƙasa tattalin arzikin yankin.

Ana kallon ƙaddamar da wannan aiki a matsayin wani misali na haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Kaduna wajen samar da ci gaba da inganta rayuwar al'umma.